Gwamnatin tarayya ta cimma yarjejeniya da ƙungiyar ƙwadago don yin amfani da kuɗin harajin VAT, wajen biyan tallafin hasken lantarki.
Ƙaramin Ministan ƙwadago Festus Keyamo wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwar bayan taron da suka gudanar, ya ce tallafin na watanni uku ne, wanda zai ba kwamitin samar da daidaito tsakanin gwamnati da ƙungiyar ƙwadagon ya gama aikin sa.
A watan Satumba ne dai aka fara anfani da sabon tsarin ƙarin kuɗin lantarkin, wanda ya samu turjiya daga ƴan Nijeriya, kuma hakan ya tilasta aka dakatar da shi na makonni biyu.
