Kwamishinar harkokin mata ta jihar Adamawa Lami Ahmad ta CE jihar ta samu rahotannin fyade 350 daga watan Mayu zuwa Oktoba, 2020.
Kwamishinar ta fadi haka ne a birnin Yola a wajen kaddamar da na’urar gano masu aikata fyade.
Lami Ahmad ta yi bayanin cewa shiru da ake yi ne ke kara yawaitar matsalolin fyade a cikin al’umma.
