Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bada izinin rushe gidan da aka samu sama da bindigogi 1,000 a cikinsa a kwaryar birnin Bauchi.
- ‘Yan sara-suka sun kai wani mummunan hari a Bauchi
- Jami’an Hisbah sun lalata kiret 260 na giya a Bauchi
Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Ladan Salihu yayin rushe gidan a ranar Laraba, ya bayyana cewa an samu bindigogin ne daure a cikin buhu tare da kayan sarki na soji da na ma’aikatan hukumar shige da fice ta kasa a wani daki cikin gidan kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.
DCL Hausa ta samu labarin cewa gwamnati ta samu bayanan sirri na irin wainar da ake toyawa a gidan ne daga wasu yan kishin kasa kuma gwamnan jihar Bauchi ya bayyana cewar sun dauki hukuncin rushe gidan ne don ya zama izina ga duk masu ajiye makamai ko yanta’adda a cikin gidajensu.
