Home Labarai Gwamnatin Bauchi ta buƙaci Sarkin Misau ya nemi yafiya

Gwamnatin Bauchi ta buƙaci Sarkin Misau ya nemi yafiya

304
0

Gwamnatin jihar Bauchi ta buƙaci Sarkin Misau Alhaji Ahmed Suleiman ya nemi gafararta saboda sakaci da aikinsa.

Kamfanin dillancin labaru na Nijeriya dai NAN, ya ruwaito cewa Gwamna Bala Muhammad ya dakatar da Sarkin tare da wasu sauran sarakunan gargajiya biyu, a kan rikicin gona da ya ɓarke tsakanin wasu Fulani makiyaya da manoma a yankin.

Babban ai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Alhaji Mukhtar Giɗaɗo ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Ya ce gwamnan ya amince da shawarar da kwamitin ya bayar na a gargaɗi sarkin tare da neman ya rubuta takardar neman afuwa.

Haka zalika gwamnatin jihar ta buƙaci masarautar Misau ta sauke magajin garin Zadawa inda rikicin ya samo asali tare da hana shi sake neman sarautar, sannan ta yi wa wasu ma’aikatan karamar hukumar Haɗawa saboda samun su da hannu waje ririta wutar rikicin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply