Home Labarai Gwamnatin Buhari bata damu da mutanen Arewa ba – NEF

Gwamnatin Buhari bata damu da mutanen Arewa ba – NEF

51
0

Kungiyar Dattawan Arewa tace Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari bata damu da ƴan Arewa, tattalin arzikinsu da kuma tsaron su ba.

Daraktan yada labaran kungiyar Dattawan Arewan Dr Hakeem Baba-Ahmed wanda ya faɗi haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya baiyana cewar sun razana matuka da wannan lamari da yake faruwa.

Kungiyar ta shaida cewa sun samu rahoto daga masu alhakin kula da aikin babbar hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano cewa aikin ba zai samu kammaluwa ba nan da shekara biyar masu zuwa.

Kungiyar dai ta koka akan yadda hanyar ta koma tarkon mutuwa ga masu zirga-zirga a kanta da kuma wurin dabdalar barayi domin sace mutane da dukiyoyinsu, sakamakon rashin saurin aikin da kuma lalacewar hanyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply