Home Sabon Labari Gwamnatin Buhari ta gaza, inji Farfesa Jega, ya koka kan rashin tsaro

Gwamnatin Buhari ta gaza, inji Farfesa Jega, ya koka kan rashin tsaro

82
0

Tsohon Shugaban Hukumar Zaben Nijeriya Farfesa Attahiru Jega ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza biya wa ‘yan kasa bukatunsu.

 

DCL Hausa ta bibiyi wata hira da jaridar DailyTrust ta yi da Jega inda a ciki ya ce “: Abin takaici Buhari ya ‘batawa mutane da dama rai. Sai dai yana da damar gyara kurakuransa, amma maganar gaskiya gwamnatinsa ta gaza. Mutane da dama na masa fatan alheri amma yanzu sun damu da alkiblar da kasar nan ke dauka.” inji Jega

 

Farfesa Jega ya kuma ce gwamnatin tarayya da ita da wasu jihohi sun gaza shi ya sa ake ci gaba da ganin tashin hankali da garkuwa da mutane a sassa daban daban na Nijeriya.

 

Farfesa Attahiru Jega wanda shi ne shugaban hukumar zabe a 2015 lokacin da Shugaba Buhari ya yi nasarar kayar da Tsohon Shugaba Jonathan, a yanzu Jegan ya ce bay a jindadin yadda al’amuran Nijeriya ke ci gaba da tabarbarewa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply