Ministan lafiya Dr Osagie Ehanire ya ce gwamnatin Nijeriya za ta kashe kudi sama da Naira bilyan 8 don sayo wasu kayayyaki 12 ga hukumar NCDC don yakar corona.
Freedom Radio Kano ta labarta cewa, Osagie Ehanire ya ce za a rarraba kayan, idan an sayo ne ga a cibiyoyin da ke gwajin cutar don kara damarar yaki da cutar.
Ministan ya ce yanzu haka wadanda suka kamu da cutar sun kai 47,299, a ya yin da mutane 33,609 suka warke, sai mutane 956 suka rasu a cikin jihohi 36 na Nijeriya.
