Gwamnatin jihar Jigawa ta ba da umurnin rufe makarantun firamare da na sakandaren jihar.
Mukaddashin babban sakataren ma’aikatar ilmi ta jihar Rabi’u Adamu ya sanar da haka ga Freedom Radio.
Rabi’u Adamu yace matakin ya shafi makarantun gwamnati da na kudi da ke fadin jihar. Sai dai babu tartibin bayanin dalilin rufe makarantun.
Amma dai tuni jama’a suka fara alakanta matakin da satar daliban da ya wakana a jihar Katsina.
