Home Labarai Gwamnatin Kaduna ta amince da buɗe makarantun gaba da sakandire 

Gwamnatin Kaduna ta amince da buɗe makarantun gaba da sakandire 

112
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince a bude makarantun gaba da sakandare a fadin jihar daga wannan Litinin 25 ga watan Junairun 2021.

A cikin wata sanarwa da DCL Hausa ta karanta dauke da sa hannun Babbar Sakatariya a ma’aikatar ilimin jihar Phoebe Sukai Yayi a madadin kwamishinan ma’aikatar, ta ce hakan ya biyo bayan rahoton kwamitin da ke sanya ido akan yaki da cutar coronavirus na jihar.

Sanarwar ta kara da cewa an amince a bude makarantun bayan nazari da kuma yadda hukumomin makarantun suka bada hadin kai tare da daukar matakan kariya daga Covid-19.

An kuma shawarci malamai da dalibai su kiyaye da dokokin corona tare da kauce wa cinkoso.

Phoebe Sukai ta kara da cewa za a ci gaba da kai ziyarar ba zata a makarantu domin tabbatar da suna bin ka’dojin da aka gindaya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply