Home Labarai Gwamnatin Kaduna ta ceto yara 160 da aka ɓoye

Gwamnatin Kaduna ta ceto yara 160 da aka ɓoye

42
0

Jami’an kwamitin kula da yaduwar cutar Covid-19 na jihar Kaduna sun ceto sama da yara 160 a wurare daban-daban, wadanda ba su da rajistar zama makaranta ko kuma wurin rainon yara a jihar.

Wasu daga cikin yaran dai sun yi kanana sosai ta yadda ba za su iya fadin daga inda suka fito ba.

Yaran da aka ceton dai, sun fito ne daga jihohi 13 na Arewaci da Kudancin Nijeriya, yayin da wasu yaran kuma sun fito ne daga kasashen Benin, Burkina Faso da jamhuriyar Nijar.

Wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mai magana da yawun gwamnan jihar ya fitar a ranar Juma’a, ya ce wuraren da aka ceto yaran, sun sabawa dokar kulle makarantu da gwamnatin jihar ta sanya a watan Disambar shekarar 2020.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply