Home Lafiya Gwamnatin Kaduna za ta kori duk jami’in lafiyar da ya ƙi zuwa...

Gwamnatin Kaduna za ta kori duk jami’in lafiyar da ya ƙi zuwa aiki

188
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi barazanar dakatar da duk wani jami’in kiwon lafiya da ya ki zuwa wajen aikin sa.

Gwamnatin jihar dai na mayar da martani ne kan sanarwar tafiya yajin aiki da jami’an kiwon lafiya a jihar suka yi, bayan cire kashi 25 na albashin ma’aikatan jihar da aka yi.

Haddadiyar kungiyoyin jami’an kiwon lafiya na jihar Kaduna dai, sun ba gwamnatin wa’adi, su mayar masu da kashi 25 na albashin da aka cire masu na watannin Afrilu da Mayu tare da bukatar gwamnatin ta samar masu kayayyakin kariya.

Saidai a wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mai ba gwamna El-Rufa’i shawara kan yada labarai ya fitar, ya ce gwamnatin ba za ta amince da abunda ta tsantsar shafawa gwamnati bakin fenti ba, a lokacin da take kokarin ci gaba da kula da bangaren lafiya tare da kare hakkokin duk ma’aikatan da suka amince za su yi aikin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply