Home Labarai Gwamnatin Kano za ta haramta tuƙa Adaidaita Sahu?

Gwamnatin Kano za ta haramta tuƙa Adaidaita Sahu?

43
0

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta sake ɓullo da dokoki kan masu tuƙa Adaidaita Sahu a jihar.

DCL Hausa ta rawaito cewa a ranar Litinin ne masu tuƙa Adaidaita Sahu na jihar suka shiga yajin aikin gargaɗi kan harajin ₦100 a kullum da gwamnatin jihar ta sanya masu.

Mai taimakawa gwamnan ta fuskar yaɗa labarai Salihu Tanko Yakasai ya sanar da matakin gwamnatin a ranar Talatar nan, a shafinsa na Twitter.

Ya ce da farko gwamnati ba ta da niyyar haramta ayyukan tuƙa baburan a jihar, amma biyo bayan abun da ke faruwa a yanzu, ya sanya dole gwamnatin za ta sake ɓullo da dokokin kula da ayyukansu.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a sanar da sabbin hanyoyin da ake buƙatar ƴan Adaidaita Sahun su riƙa ayyukansu da kuma sabbin matakan da za a ɗauka.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply