Home Labarai Gwamnatin Kano za ta raba titunan jihar da mabarata da yan talla

Gwamnatin Kano za ta raba titunan jihar da mabarata da yan talla

31
0

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na raba titunan jihar daga masu gararanba da sunan bara ko talla.

Kwamishiniyar harkokin mata ta Jihar, Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayyana hakan lokacin da take zantawa da manema labarai a ofishinta a Kano ranar Litinin.

Ta ce tuni shirye-shirye suka yi nisa wurin ganin an sami nasarar aiwatar da shirin, musamman kan wadanda suke gararanbar ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Kwamishiniyar ta ce gwamnatin jihar ta tattauna da masu ruwa da tsaki a fadin jihar, ciki har da shugabannin al’umma da na addini daga masarautun jihar guda biyar domin lalubo bakin zaren matsalar.

Zahra’u ta kuma ce jihar ta fitar da kudi miliyan ₦4m domin fara aikin ka’in da na’in.

Kazalika, Kwamishiniyar ta ce a kwanan nan ma’aikatarta ta karbi wasu rukunin almajirai biyu da aka dawo da su Kano daga jihar Kaduna.

Ta kuma ce nan ba da jimawa ba za a tsugunar da wasu mutane 47 maza da mata dake gararanba a kan tituna domin gyaran hali sannan a raba su da titunan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply