Home Labarai Gwamnatin Katsina ta hana malamai yin amfani da WhatsApp Group

Gwamnatin Katsina ta hana malamai yin amfani da WhatsApp Group

115
0

Gwamnatin jihar Katsina ta haramta wa malamai da sauran ma’aikatan makarantun jihar yin amfani da kafafen WhatsApp wajen yaɗa labarai.

Gwamnatin ta ce yin amfani da kafar na janyo rashin biyayya tsakanin malaman da ma’aikatan.

Bayanin hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da aka raba wa makarantun ɗauke da sa hannun Muhammad Dikko na sashen tabbatar da ingancin ilimi na jihar, inda ya yi gargaɗin hukunci mai tsanani ga waɗanda suka saɓa umarnin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply