Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya ce ma’aikatar sufurin jihar KTSTA ta kashe sama da Naira miliyan ₦70m wajen gina sabuwar tashar motoci a garin Malumfashi.

Gwamnan ya faɗi haka ne lokacin ƙaddamar da tashar mota, yana mai cewa ma’aikatar ta samu kuɗin ne ta hanyar kuɗin shigar da take samu.
Wannan dai na daga ƙoƙarin da ma’aikatar ke yi na farfaɗo harkokin sufuri a jihar.
Gwamna Masari ya ce gina tashar motar, a nuna yadda ƙoƙarin farfaɗo da ɓangaren sufurin ya fara bada sakamako mai kyau.
Kwamishinan ayyuka, sufuri da gidaje na jihar Alhaji Tasi’u Ɗanɗagoro ya ce sabuwar tashar ta ƙunshi ofisoshi, banɗaki, masallacin maza da mata da sauran gine-gine.
