Home Labarai Gwamnatin Katsina ta kashe sama da ₦22m wajen yaƙi da gobara

Gwamnatin Katsina ta kashe sama da ₦22m wajen yaƙi da gobara

105
0

Kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da lamuran cikin gida na jihar Katsina Abdulkarim Sirika ya bayyana cewa kimanin mutane 50 ne suka rasa rayukansu sakamakon tashin gobara a jihar ta Katsina cikin wannan shekara.

Sirika ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a Katsina inda yake cewa lamarin ya auku ne daga watan Janairu zuwa Disamban wannan shekarar.

Ya kuma ce jami’an kashe gobara sun ceci rayukan mutane 95 da dukiya ta miliyoyi a ɗan tsakanin.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta kashe kudi har ₦10.7m wajen siyan kayan kashe gobara, sinadarai da kaki ga jami’an kashe gobarar tare da sauran wasu aikace-aikace da aka yi wa hukumar da suka haura ₦22m.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci baga da ba gwmanati tare da hukumar kashe gobarar hadin kai don ci gaba da kiyaye hadurran wuta da kuma ciyar da jihar gaba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply