Home Labarai Gwamnatin Katsina ta maka Mahadi Shehu kotu, an aike masa sammaci

Gwamnatin Katsina ta maka Mahadi Shehu kotu, an aike masa sammaci

267
0

Babbar Kotun Majistare ta daya da ke Katsina ta ba da umurnin lika sammanci a gidan Mahadi Shehu da harabar gine-ginen wuraren kasuwancinsa daban-daban dake Kaduna.

Babban Majistare Abdu Ladan ya bada umurnin hakan ne a sakamakon ci gaba da guje-gujen da Mahadi Shehu ke yi na kin yarda ya yi tozali da Masinjan da Kotun ta tura gidansa da wuraren sana’o’in shi dake Kaduna domin ya sada shi da sammacin hannu da hannu.

Tun farko Babban Majistaren ya amince da rokon da lauyan dake tsaya ma Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Earnest Abunadike ya shigar na neman a dauki mataki na gaba tun da dai jami’an Kotun sun nemi wanda ake tuhumar ruwa jallo ba su gan shi ba.

Haka kuma sai da Kotun ta umurci Masinjan da ya kai sammacin bai ga Mahadin ba, da ya je Babbar Kotu ya cika takardar rantsuwa ta kotu dake tabbatar da cewa, lalle ya je neman Mahadi duk inda ake sa ran ganin sa amma ba a gan shi ba.

Yanzu dai Kotun ta tsaida ranar Talata, 2 ga watan 11 domin ci gaban shari’ar.

Wata majiya kusa da Kotun ta ce a ranar Talatar idan har Mahadi ya kasa bayyana a gabanta to Kotun za ta iya ba da waranti a kamo shi a duk inda yake.

Haka kuma Kotun za ta iya ci gaba da sauraren shari’ar har ta kai ga yanke hukunci kuma hukuncin duk da ta zartas zai hau kansa duk ranar da ya zo hannu.

Gwamnatin Jihar Katsina gurfanar da Mahadi Shehu a gaban kotu ne tana tuhumar sa da yin takardun bogi da kuma tunzura jama’a da su yi ma Gwamnati tawaye.

Bayanai sun ce jami’an Kotu sun lika takardun sammacin masu dauke da bayanin irin tuhumar da ake yi wa Mahadi da kuma ranar da Kotun ke neman sa.

An hango takardun sammancin manne a Dialogue Building dake Titin Sultan, da Dialogue Institute, Ali Akilu da kuma Dialogue Hospital and Pharmacy dake Titin Isa Kaita dukkan su mallakin Dan Nijeriyar nan, dan asalin Jihar Katsina, haifaffen Kofar sauri mai suna Mahadi Shehu.

Dama dai a faya-fayan bidiyon da Mahadi Shehu ke fitarwa ta kafofin sadarwarvzamani, ya sha rokon gwamnati da sauran mutane da ya zarga da badakalar kudin jihar, da su kai shi kotu domin a san biri a san gata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply