Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira bilyan 2.7 don sayo takin zamani

Gwamnatin Katsina za ta kashe Naira bilyan 2.7 don sayo takin zamani

115
0

Gwamnatin jihar Katsina ta amince da sayo tan 30,000 na takin zamani don sayarwa ga manoma a farashi mai sauki.

Kwamishinan kasafin kudi na jihar Faruq Lawal Jobe ya sanar da cewa gwamnatin za ta kashe kudi Naira milyan dubu biyu da milyan bakwai (2.7 billion) don sayo takin ga manoman daminar bana.

Ya sanar cewa za a sayar da takin ne kan kudi Naira 4,000 ga duk buhu.

To sai dai, masu aharhi kan lamirran yau da kullum na takokin yadda noma zai kasance a daminar bana ganin yadda ‘yan bindiga ke kai hari a garuruwa mabambanta na jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply