Home Labarai Gwamnatin Kebbi ta ware ₦3bn don biyan hakƙoƙin tsaffin ma’aikata

Gwamnatin Kebbi ta ware ₦3bn don biyan hakƙoƙin tsaffin ma’aikata

120
0

Gwamnatin jihar Kebbi ta ba bori kai ya hau, kan barazanar yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon jihar suka yi barazanar tafiya, ta hanyar amincewa da sakin Naira biliyan ₦3bn don biyan tsaffin ma’aikatan jihar hakƙoƙinsu.

A ranar 11 ga watan Disambar bara ne dai, shugaban ƙungiyar Ƙwadago na jihar NLC Umar Halidu Alhassan da na ƙungiyar ƴan kasuwa TUC Ɗanladi Aliyu Dabai suka ba gwamnatin jihar wa’adin zuwa 1 ga watan Janairun bana, ta biya tsaffin ma’aikatan hakƙoƙinsu ko kuma su tsunduma yajin aiki.

Kwamishinan kuɗi na jihar Ibrahim Muhammad Augie ya sanar da amincewa da fitar da kuɗin, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce daga cikin kuɗin, za a ware Naira biliyan ₦2bn domin tsaffin ma’aikatan gwamnatin jiha, sai kuma Naira biliyan ₦1bn na ma’aikatan ƙananan hukumomi da malamansu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply