Home Labarai Gwamnatin Kwara ta umarci ma’aikata su koma aiki

Gwamnatin Kwara ta umarci ma’aikata su koma aiki

91
0

Gwamnatin jihar Kwara ta umarci ma’aikatanta da su koma bakin aikinsu.

Umarnin na cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar Modupe Oluwole ya fitar a Birnin Ilorin, ranar Talata.

Shugaban ma’aikatan ya bada tabbacin gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da walwalar ma’aikatan jihar.

DCL Hausa ta ruwaito cewa, a ranar Litinin ne dai wata kotun ma’aikata ta dakatar da ƙungiyoyin ƙwadagon jihar tafiya yajin aiki saboda rashin samun daidaito kan tsarin mafi ƙarancin Albashi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply