Gwamnan jihar Nassarawa Abdullahi Sule ya bayyana kudirin gwamnatinsa kan shirin da take na fara biyan sabon tsarin mafi karancin albashi ga ma’aikatan da suke matakin aiki na 6 zuwa kasa.
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin tarbar kungiyar mata ƴan kasuwa ta kasa a gidan gwamnatin jihar.
Ya kuma bayyana yadda ma’aikata masu matakin aiki na 7 zuwa sama suka dade suna morar tsarin tun daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata.
