Home Labarai Gwamnatin Neja ta kori ma’aikata 80

Gwamnatin Neja ta kori ma’aikata 80

85
0

Gwamnatin jihar Neja ta kori ma’aikata 80 daga aikin gwamnati bisa zarginsu da dora kansu bisa albashin da ba su kai matsayin ba.

Shugabar ma’aikatan jihar Salamatu Abubakar wadda ta bayyana haka ga manema labarai a birnin Minna, ta ce korar wadannan ma’aikatan ya zo ne bayan amincewa da majalisar zartaswar jihar ta yi a taron da ta gudanar ranar Alhamis.

Shugabar ma’aikatan ta ce kwamitin da gwamna Abubakar Sani Bello ya kafa don bincikar badakalar ne ya gano su.

Salamatu ta ce mutanen sun samar wa kansu alawus-alawus na babu gaira babu dalili, da hawa bisa albashin da ba su kai matakin ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply