Gwamnatin Nijeriya ta ce ta fara wani bincike na yadda za ta yaki kudan-tsando domin inganta lafiyar dabbobi a jihar Gombe.
Ma’aikatar aikin gona ta kasa ta sanar da hakan ta hannun babban jami’in yaki da kudan-tsando na ma’aikatar Duchi Dang a birnin Gombe.
Duchi Dang, ya ce zaba kwashe kwanaki 5 zuwa 7 ana gudanar shirin yakar kudan-tsando hadin guiwa da jami’ai daga kananan hukumomin jihar Gombe.
