Home Coronavirus Gwamnatin Nijeriya na shirin sake kulle wasu kananan hukumomi

Gwamnatin Nijeriya na shirin sake kulle wasu kananan hukumomi

151
0

Kwamitin yaki da annobar Corona virus da fadar Shugaban kasa ta kafa yace akwai yiyuwar gwamnatin kasar ta kara sanya dokar kulle ga wasu kananan hukumomi 18 domin dakile ci gaba da yaduwar cutar corona.

Kananan hukumomin guda 18 dai suke da kaso 60% na yawan wadanda suka kamu da wannan annoba.

Shugaban kwamitin Mr Boss Mustapha ne ya bayyana haka a wani taro da suka yi da shugaba Buhari dangane da ci gaban da kasar ke samu kan yaki da annobar corona virus.

A karshe ya bayyana cewa sanya wannan doka a wadannan kananan hukumomin nada muhimmancin gaske musamman ma ga gwamnatocin jihohin da abin ya shafa, inda za su sami damar gudanar da gwaje-gwaje da kuma bada kulawa ga masu dauke da cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply