Gwamnatin Nijeriya ta ayyana Talata, 25 ga Agusta, 2026, a matsayin ranar hutu ta kasa domin bikin Eid ul-Mawlud, wato zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, cikin wata sanarwa da babbar sakatariyar ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar ranar Juma’a.
Tunji-Ojo ya taya Musulman Nijeriya da na sauran sassan duniya murnar wannan rana, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi tunani kan darussan tausayi, tawali’u da hidima ga al’umma da ake dangantawa da rayuwar Annabi Muhammad (SAW).
Ya ce: “Kowace ranar Eid ul-Mawlud tana ba mu damar tsayawa mu yi tunani tare da daukar darasi daga rayuwar da aka gina kan tausayi, tawali’u da hidima ga wasu.
“Wadannan dabi’u su ne kasarmu ke matukar bukata a yanzu fiye da kowane lokaci, kuma ina kira ga kowane dan Nijeriya, ba Musulmai kadai ba, da ya yi tunani a kansu.”
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da hadin kan kasa, yana mai cewa kiyaye hadin kai nauyi ne da ya rataya a kan kowa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ya bukaci jama’a su gudanar da bikin cikin natsuwa da mutunta juna, tare da yi wa al’ummar Musulmi fatan samun Eid mai cike da farin ciki da zaman lafiya.
Tunji-Ojo ya kuma sake jaddada kudurin gwamnatin yanzu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da dorewar zaman lafiya a fadin kasar.
