Home Labarai Gwamnatin Nijeriya ta bada hutun babbar Sallah

Gwamnatin Nijeriya ta bada hutun babbar Sallah

136
0

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayyana ranakun Alhamis 30 da Juma’a 31 ga watan Yuli a matsayin ranakun hutun bikin babbar Sallah.

Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikatar Geogina Ehuriah ta fitar a ranar Talata.

Ministan ya yi kira ga al’ummar musulmi da su yi koyi da dabi’ar nuna son juna, zaman lafiya, da sadaukarwa kamar yadda Annabi Muhammad S.A.W ya koyar.

Aregbisola ya kuma yi kira garesu, da su yi amfani da wannann dama wajin yiwa kasar addu’a, musamma a wanna lokaci da ake fama da matsalar Covid-19.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply