Home Labarai Gwamnatin Nijeriya ta buɗe sansanin NYSC

Gwamnatin Nijeriya ta buɗe sansanin NYSC

125
0

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da sake buɗe sansanin horas da Matasa masu yi wa ƙasa hidima NYSC a faɗin ƙasar.

Ministan ci gaban matasa da wasanni Sunday Dare, ya bayyana haka a wani saƙon twitter da ya wallafa, da safiyar ranar Alhamis.

A ranar 18 ga watan Maris ne dai gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe sansanonin horas da matasan, biyo bayan ɓarkewar cutar Covid-19 a ƙasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply