Home Labarai Gwamnatin Nijeriya ta haramtawa jami’anta halartar taruka

Gwamnatin Nijeriya ta haramtawa jami’anta halartar taruka

146
0

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta dakatar da duk wasu tafiye-tafiyen halartar taron da bai da muhimmanci ga jami’an gwamnati har sai abunda hali ya yi.

Sakataren gwamnatin kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar Covid-19 Boss Mustapha ya fadi haka a Abuja, lokacin taron kwamtin karo na 50.

Ya kuma ce duk wani taron da ya wuce mutum hudu a hukumomi to a rika gudanar da shi ta hanyoyin zamani daga ofisoshi.

A cewar Mustapha, dole ne ‘yan Nijeriya su kasace a ankare don daukar matakan yaki da cutar Covid-19 don kaucewa da-na-sani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply