A ƙoƙarinta na samar da maganin Covid-19 a gida, gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamitin bincike kan magungunan gargajiya.
Ministan kimiyya da fasaha Ogbonnaya Onu, wanda ya ƙaddamar da kwamitin, ya ce akwai buƙatar samar da maganin cutar da ma riga-kafinta cikin gaggawa saboda yadda take zama barazana ga lafiyar ƴan Nijeriya da ma tattalin arziƙin ƙasa.
Onu, ya ce kwamitin wanda ya ƙunshi masana kimiyya da malaman kimiyyar ƙasar, za su tantance iƙira8masu bincike, masana kimiyya da masu magungunan gargajiya da ke cewa sun samar da maganin cutar.
