Home Labarai Gwamnatin Nijeriya ta maka manoma 70,000 kotu a jihar Kebbi

Gwamnatin Nijeriya ta maka manoma 70,000 kotu a jihar Kebbi

91
0

Ma’awiyya Abubakar Sadiq

Yanzu haka kusan manoma dubu saba’in ne a jihar Kebbi gwamnatin tarayya ta tusa keyarsu kotu biyo bayan kasa biyan bashin tallafin noma da suka amfana da shi a shekarar 2015, bayan kaddamar da shirin noman shinkafa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a jihar.

Manoman dai na shinkafa da alkama a jihar Kebbi sun amfana da tallafin kudi ne da suka kai kimanin naira biliyan 17, karkashin shirin (Anchor Borrower Scheme) da za su biya ba tare da kudin ruwa ba. Sai dai daga cikin manoman dubu saba’in manoma dari biyu ne kawai suka biya bashin.

Tallafin dai ana ganin gwamnatin ta bayar da shi ne don inganta harkokin noma musamman na shinkafa a jihar Kebbi. To amma sai dai a bangare daya jam’iyyar adawa a jihar na zargin muzgunawa ga manoman jihar, inda suke cewa tallafin bai amfanar da jihar komai ba.

Amma, wani bincike na nuna kafin zuwan tallafin manoman shinkafa a jihar Kebbi na samar da Tan dubu saba’in, ya yin da a shekarar 2016 bayan samun tallafin aka samar da Tan miliyan daya da dubu dari biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply