Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Gwamnatin Nijeriya ta raba bilyan 265 na shirin samar da gidaje

Gwamnatin Nijeriya ta raba bilyan 265 na shirin samar da gidaje

140
0

Bankin ba da lamunin gidaje na “Mortgage” ya sanar cewa tuni ya rigaya ya rarraba kudin da suka kai darajar Naira bilyan 265 ga wadanda suka shiga tsarin samun gidaje.

Bankin ya sanar cewa wadanda ke da bukatar gidajen sun kara yawa zuwa milyan 5.1 sabanin dubu 570,000 da ke cikin tsarin.

Shugaban bankin Ahmad Musa Dangiwa ya ce jimillar kudin da aka rarraba, na nufin an samu karin Naira bilyan 112 sama da abin da ke da akwai a 2017.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply