Gwamnatin Nijeriya ta ce ta raba kuɗi Naira Biliyan ₦66.5 na tallafin Covid-19 ga jihohin da suka cika ƙa’idar yaƙi da cutar.
Ministar kuɗi da kasafi Zainab Ahmad ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatarta Hassan Dodo ya fitar a Abuja, tana mai cewa an raba kuɗin ne ga jihohi 35 da suka cika sharudɗan yaƙi da cutar.
Sanarwar ta ce ko wace jiha ta samu Naira biliyan ₦1.9bn daga cikin kuɗin waɗanda bashi ne daga ƙungiyar ci gaba ta duniya IDA, kuma jihar Rivers ce kaɗai bata cika ƙa’idar amfana da kuɗin ba.
