Home Sabon Labari Gwamnatin Nijeriya ta umarci ma’aikata su koma bakin aiki ranar Litinin

Gwamnatin Nijeriya ta umarci ma’aikata su koma bakin aiki ranar Litinin

113
0

Gwamnatin Nijeriya ta sanar a ranar Larabar nan cewa ta amince ma’aikatun gwamnati a fadin kasar su koma bakin aiki daga ranar Litinin mai zuwa. Sai dai ta ce ma’aikata kalilan ya kamata a su koma ba wai kowa da kowa ba kuma wadanda za a umarci su koma din za a duba matakin albashinsu kafin a sahale musu komawa bakin aiki.

Shugaban Kwamitin Kula da Coronavirus Dakta Sani Akiyu ya ce bankuna da ma’aikata masu gine-gine da masana’antu za su iya bude su ma daga ranar Litinin din. Sai dai gwamnati ta ce an amince bankuna su yi aiki a tsakanin karfe takwas na safe zuwa karfe biyu na rana, kamar yadda jaridar DailyTrust at ruwaito. 

Sai dai ya ce gwamnati za ta fito da tsarin auna zafin jikin ma’aikata kafin a barsu shiga wurin aiki kuma za a hana taron mutane fiye da ashirin a wuri guda.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply