Home Labarai Gwamnatin Nijeriya za ta ci bashin $22.8bn

Gwamnatin Nijeriya za ta ci bashin $22.8bn

71
0

Gwamnatin tarayya ta nemi amincewar Majalisar dattawa domin ciyo bashin Dala biliyan $22.8 domin ayyukan ci gaba.

Ministar kuɗin Nijeriya, Zainab Ahmed

Ministar kuɗi Zainab Ahmed ta gabatar da buƙatar a gaban kwamitin Majalisar kan harkokin bashi.

Ta ce bashin na cikin tsarin rance na shekarar 2016 zuwa 2018 wanda aka tsara don ayyukan tituna, da layukan dogo, da hasken lantarki, da noma da dai sauran su.

A cewar Ministar, bashin zai taimaka wajen samar da rance da ba ruwa ga ƙanana da matsakaitan sana’o’i a cikin ƙasar.

Ta ƙara da cewa a halin yanzu matsalar samar da kuɗaɗen shiga shi ke damun Nijeriya amma ba wai bashi ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply