Gwamnatin Nijeriya ta jaddada aniyarta ta kawo karshen yin bahaya a fili da ma inganta hanyar samar da ruwan sha a ilahirin jihohin kasar nan.
Ministan albarkatun ruwa, Sulaiman Adamu ne ya bayyana haka a cikin wani sako da ya aike da shi a wani taron wayar da kai da ya gudana a garin Owerri na jihar Imo.
Sulaiman Adamu ya ce ma’aikatar albarkatun ruwa ta gano irin muhimmiyar gudunmawar da hukumar wayar da kan jama’a ke bayarwa wajen kawo ci gaban al’umma.
