Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Gwamnatin Nijeriya za ta samar da lantarki ga gidaje milyan 5

Gwamnatin Nijeriya za ta samar da lantarki ga gidaje milyan 5

97
0

Ma’aikatar wutar lantarki ta tura wani kaso a cikin kudade fiye da Naira tiriliyon 2.3 a shirin nan na bunkasa tattalin arzikin kasa da ke karkashin ofishin mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo domin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga akalla gidaje milyan 5 a fadin Nijeriya.

Karamin ministan makamashi Goddy Jedy Agba ne ya bayyana haka a wurin taron kaddamar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana na Unguwar Karu da ke Abuja.

Mista Goddy ya ce gwamnatin tarayya ta bullo da hanyoyin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a karkashin shirin hukumar rarraba wutar lantarki tare da hadin guiwar bankin duniya, a yunkurinsu na sama wa gidaje dubu 300 da ‘yan kasuwa dubu 30 hasken wutar lantarki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply