Home Labarai Gwamnatin Nijeriya za ta yi wa ASUU kishiya

Gwamnatin Nijeriya za ta yi wa ASUU kishiya

126
0

A daidai lokacin da ƙungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ke ci gaba da yajin aiki tsawon wata goma, gwamnatin Tarayya ta fara shirin rajistar wata ƙungiyar da za ta zama kishiyar ASUU.

Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya bayyana haka a Abuja lokacin da sabuwar ƙungiyar malaman jami’o’i ta CONUA mai adawa da ASUU, ƙarƙashin jagorancin Dr Niyi Sunmonu suka kai masa ziyara.

Ngige ya bayyana rashin jin daɗinsa ga yajin aikin na ASUU yana mai cewa yajin aikin ya yi illa sosai ga ci gaban ilimin ƙasar.

A jawabinsa tun da farko, Sunmonu, ya ce ƙungiyar CONUA na samun goyon bayan malaman jami’o’in da ke yin rajista da ita tun bayan ɓullo da ita a watan Fubrairun 2018.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply