Gwamnan jihar Plateau Simon Bako Lalong, ya ce gwamnatin jihar ta kashe kudi Naira milyan 366.5 don yaki da cutar corona a jihar.
Gwamnan Lalong ya gurta haka ne a taron masu ruwa da tsaki kan wayar da kan al’umma dangane da cutar corona a birnin Jos.
Ya ce gwamnatin jihar ta kuma kafa kwamitin shirye-shiryen sake bude makarantu a jihar, biyo bayan rufe su da aka yi ta dalilin cutar corona.
