Home Lafiya Gwamnatin Sakwato ta raba motoci 30 ga jami’an tsaro

Gwamnatin Sakwato ta raba motoci 30 ga jami’an tsaro

156
0

Gwamnatin jihar Sakkwato ta rarraba motoci sama da talatin ga jami’an tsaro don kara masu kaimi ga ayukkan su.

Gwamnatin ta ce yin hakan wani mataki ne na yakar ‘yan ta’adda da suka addabi al’ummar jihar.

DCL Hausa ta ba da rahoton cewa motocin kirar Hillux da Golf an rarraba su ne ga jami’an tsaro da ke jihar domin saukaka masu ga gudanar da aikin sintiri don kakkabe masu aikata miyagun laifuka.

Gwaman jihar Aminu Tambuwal yace baya ga motocin da aka samar za a samar da wata cibiya ta musamman da za a rika Kiran waya don shaida inda ‘yan ta’adda suke kan kaddamar da hari, inda jami’an tsaron za su kai daukin gaggawa.

Idan dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne ‘yan ta’adda suka kai wani hari a gabashin jihar Sakkwato da ya yi sanadiyar mutuwar mutane saba’in da hudu lamarin da ya haifar da daukar wannan matakin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply