Home Labarai Gwamnatin Sokoto ta yi watsi da karatun ‘ya’yan Fulani

Gwamnatin Sokoto ta yi watsi da karatun ‘ya’yan Fulani

116
0

Yanzu haka sarakuna da shugabannin fulani na kokawa dangane da yadda gwamnatin jihar Sakkwato ta yi watsi da karatun ‘ya’yan makiya a jihar.

Alhaji Nasiru Sarkin Fulani, wanda shi ne Sarkin Fulanin Sokoto, na daga cikin shugabannin fulani a jihar da suka tabbatar da cewa dukkanin tsarin da aka yi na samar da ilmi ga ‘ya’yan makiyaya an sa k’afa an shure shi.

Ya ce Kusan a mako, sau d’aya za ka ji malami ya shiga a makaranta, haka kuma babu kayan da aka tanada ga malamai da za su rik’a shiga don koyar da ‘ya’yan makiyaya.

Alhaji Nasiru yace wasu yankuna da dama da makiyaya suke, babu ma makarantun, sannan babu wani saka ido da gwamanati ke yi na koyar da ‘ya’yan makiyayan.

Kokarin jin ta bakin hukumomin da ke kula da ilimin ‘ya’yan makiyaya a jihar da DCL Hausa ta yi, ya faskara domin sun kasa cewa uffan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply