Home Labarai Gwamnatin tarayya bata kara wa’adin ma’aikatan da za su aje aiki bana...

Gwamnatin tarayya bata kara wa’adin ma’aikatan da za su aje aiki bana ba

159
0

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce bata amince da kara wa’adin ma’aikatan da za su ajiye aiki a shekarar 2020 ba.

Cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai a Ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Olawunmi Ongunmosunle ya fitar a Abuja, ya Ambato shugabar ma’aikatan Dr Folasade Yemi-Esan na cewa babu wata sanarwa irin wannan da ta fito daga ofishinta.

A cewarta, wannan sanarwa ta zama wajibi, duba da yadda ake yada wani labarin karya da ake cewa ya fito daga ofishinta, wai an kara wa’adin ma’aikatan da za su aje aiki a bana.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply