Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Gwamnatin tarayya ta raba kayan aiki ga manoma a Jigawa

Gwamnatin tarayya ta raba kayan aiki ga manoma a Jigawa

102
0

Ministan Noma da raya karkara Sabo Nanono ya raba kayan aikin gona da Iri ga manoman da annobar ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.

Nanono wanda ya kaddamar da raba kayan a ranar Asabar, ya bayyana cewa an yi hakan ne don tallafa wa mutanen da ibtila’in ya afkawa a ƙananan hukumomin Auyi da Hadejia.

Ministan ya bayyana cewa hakan zai kara habbaka noma a yankunan da kuma samar da wadataccen abinci ga kasa baki daya.

Abubuwan da aka raba wa manoman sun hada da Irin shinkafa, masara, alkama gyada da kuma irin tumatir, kayan aikin sun hada da injin banruwa, kayan aikin noman rani, kan famfo masu amfani da hasken rana, injin casar masara da sauransu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply