DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeBabban Labari Gwamnatin Tinubu za ta samar da wutar lantarki ta awa 24 a...

Gwamnatin Tinubu za ta samar da wutar lantarki ta awa 24 a Legas, Abuja, Kano da wasu birane

Gwamnatin Nijeriya ta himmatu a shirin kafa wasu makamashi na musamman da ake kira Energy Zones a manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu, domin samar da wutar lantarki na tsawon sa’o’i 24 a wuraren da ake da matuƙar buƙatar ta.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an bayyana shirin ne bayan wata ganawa da Ministan lantarki, Joseph Tegbe ya yi da shugabannin wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki a Abuja.

Ganawar ta kasance wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin Tinubu na samar da ingantacciyar wutar lantarki ga ’yan Nijeriya, musamman a yankunan da ake samun yawan amfani da lantarki saboda harkokin kasuwanci da masana’antu in ji wata sanarwar da Adeola Labzy, mai ba Ministan lantarki shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a ta fitar.

A cewarta, za a kafa makamashin ne a wasu manyan yankuna da suka haɗa da Legas, Abuja-Kaduna-Kano da Enugu da kuma Port Harcourt.

Ministan ya ce matakin wani ɓangare ne na tsarin da ma’aikatar lantarki ke amfani da shi wajen tunkarar matsalolin da suka addabi ɓangaren samar da wutar a Nijeriya.

Ya bayyana cewa matsalar wutar lantarki a Nijeriya ba ta tsaya ne kawai kan yawan wutar da ake samarwa ko hanyoyin isar da ita ba, domin akwai kuma ƙalubalen yadda ake karɓar wutar da kuma rarraba ta ga masu amfani.

A cewarsa, Energy Zones ɗin da ake shirin kafawa za su taimaka wajen rage wannan gibi, tare da buɗe damar amfani da wutar lantarki ga manyan ’yan kasuwa da masana’antu.

Ministan ya kuma ce tsarin zai taimaka wajen ƙarfafa kudaden shiga da karɓar kuɗaɗen wutar lantarki daga kamfanonin rarraba wutar wato DisCos.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin na da niyyar ƙara gine-ginen ababen more rayuwa da suka shafi wutar lantarki a wuraren da ake da yawan buƙata.

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa samar da wutar lantarki yana tafiya daidai da yadda ake hasashen buƙatar lantarki a yayin da tattalin arzikin ƙasar ke ci gaba da bunƙasa.

Ministan ya danganta shirin da manufar Renewed Hope Agenda ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wadda ta sanya samar da ingantaccen makamashi cikin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki.

Ya ce ingantacciyar wutar lantarki na da muhimmiyar rawa wajen haɓaka masana’antu, ƙirƙirar ayyukan yi da kuma bunƙasa harkokin kasuwanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata