Shugaban ƙungiyar gwamnonin Nijeriya kuma gwamnan jihar Ekiti Dr Kayode Fayemi, ya bayyana goyon bayan gwamnonin ƙasar 36 na ba ɓangaren shari’a cikakken ƴanci.
Fayemi wanda ya bayyana ɓangaren shari’a a matsayin ginshiƙin demokraɗiyya, ya ce wajibi ne a yi wasu gyare-gyare a ɓangaren da za su tabbatar da bin doka da oda a ƙasar.
Shugaban na NGF wanda ya yi magana a lokacin da ya tarbi zaɓabɓen shugaban ƙungiyar lauyoyi na ƙasa Olumide Akpata a Ado Ekiti, ya ce babban abun da gwamnonin suka ba fifiko shi ne ba ɓangaren shari’a ƴancin cin gashin kansa, kuma suna ƙoƙarin ganin aiwatar da hakan.
