Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Gwamnoni sun yi taro kan yadda za a rage haraji

Gwamnoni sun yi taro kan yadda za a rage haraji

113
0

Kungiyar gwamnonin Nijeriya ta yanke shawarar ta aiwatar da wasu sabbin shirye-shirye na yadda za a rage kudaden haraji ga ‘yan kasuwa da masu biyan kudaden haraji a fadin jihohin kasar baki daya saboda matsalolin da ake fuskanta.

Shugaban kungiyar gwamnonin gwamnan jihar Ekiti Mista Kayode Fayemi ne ya sanar da haka a taron da kungiyar ta gudanar ta intanet karo na 16.

Fayemi ya ce gwamnatocin jihohin ta karkashin kudaden shiga da suke samu, za su tabbatar da aiwatar da rage kudaden haraji a jihohinsu.

Kazalika, ya ce za a rage kudaden haraji ga mutanen da suke biyan haraji a kasar nan a sabuwar shekara mai zuwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply