Kungiyar gwamnonin Nijeriya ta ce ta shirya domin tunkarar shugaban kasa Muhammad Buhari bisa karin kwana-kwanan nan na man fetur da wutar lantarki.
Jaridar Daily Nigerian ta rawito cewa a ranar 2 ga wannan watan na Satumba ne kamfanin kula da kasuwancin fetur PPMC ya sanar da karin kudin mai zuwa Naira 151.56 a duk lita.
Da ya ke karin haske ga manema labarai, gwamna Muhammad Badaru na Jigawa, ya ce wannan karin ya sosa ran gwamnonin kasar, ganin yadda kowa ke ta wayyo-wayyo.
