Home Labarai Gwamnonin APC na goyon bayan Ngozi a shugabancin WTO

Gwamnonin APC na goyon bayan Ngozi a shugabancin WTO

135
0

Shugaban kungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya yi kira ga kasashen da ke hukumar kasuwanci ta duniya, da su goyi bayan ‘yar takarar Nijeriya Dr. Ngozi Okonjo Iweala a matsayin babbar daraktar hukumar.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba, Bagudu, ya ce babban dalilin kafa hukumar shi ne don samar da kyakkyawan tsarin kasuwancin da babu rudani a ciki.

A cewarsa, matsalolin da cutar coronavirus ta haifar ga kasuwancin duniya, wata ‘yar manuniya ce ga bukatar da ke akwai na samar da kyakkyawan tsarin kasuwanci.

Tseren neman wanda zai sake zama shugaban hukumar zai dauki sabon salo, a daidai lokacin da ‘yan takara takwas, daga nahiyoyi hudu za su gabatar da kansu a gaban wakilan hukumar domin bayyana manufofinsu a makon nan.

‘Yan takarar, wadanda suka kunshi maza biyar da mata uku, za su fara gabatar da kan su ne a gaban wakilan kasashe 164 daga yau Laraba 15 ga wata zuwa 17 ga watan Yuli.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply