Home Sabon Labari Gwamnonin Arewa Sun Sha Alwashin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Jihohinsu

Gwamnonin Arewa Sun Sha Alwashin Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Jihohinsu

69
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”2qd17ubbno” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”ujrygv5zd” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”o1a8p3u6qh” animation_delay=”0″]

An kammala taron gwamnonin jihohin Arewa a fadar gwamnati ta Sa Kashin Ibrahim da ke Kaduna a alhamis da ta gabata da yanke shawarar hada karfi wuri guda don kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar yankin.

 

Taron ya tattauna a kan muhimman batutuwa da suka shafi jihohin musamman bunkasa aikin gona da kyautata tsaro a yankin. Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Filato, Mista Simon Lalong, ya karanta jawabin bayan taron.

Cikin abubuwan da aka cimmawa a karshen taron sun hada da yadda za su kawo karshen matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa duk da kokarin da gwamnatocin ke ta yi a kowanne mataki, inda kungiyar ta yanke shawarar ci gaba da daukar kwararan matakai don magance lamarin.

Jaridar Daily Post ta ce jawabin bayan taron ya jaddada kudirin kungiyar na bunkasa tattalin arziki, da zamantakewa a Arewa. Taron ya kuma amince da wani tsari na bunkasa kiwo da karfafa wa sauran jihohin da ba su rungumi shirin ba, su kokarta su yi. Har gwamnan jihar Zamfara matawalle ya bayyana nasarar da ya samu ta wanzar da zaman lafiya a fadin jiharsa.

 

 

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply