Home Sabon Labari Gwamnonin Arewa sun yi tir da satar ɗaliban Kagara

Gwamnonin Arewa sun yi tir da satar ɗaliban Kagara

27
0

Gwamnonin Arewacin Nijeriya sun yi tir da satar dalibai da ma’aikatan Kwalejin Kimiyya ta Kagara a jihar Neja, da suka bayyana a matsayin wata makarkashi ta gurgunta neman ilimi a yankin.

Wata sanarwa da shugaban kungiyar gwamnonin kuma Gwamnan jihar Plateau Simon Lalon ya fitar a birnin Jos ranar Laraba, ya ce gwamnonin sun nuwa damuwarsu da yin tir da satar yaran wadanda ba su tsare wa kowa komai ba, in banda kokarin da suke na neman ilimi.

Sanarwar ta bayyana harin da cewa wani mataki ne, na gurgunta sanya yara makaranta musamman a yankin Arewa da ke fama da matsalar jahilci, saboda yadda aka ga yankin na samun ci gaba wajen sanya yara makaranta, sakamakon kokarin da gwamnatoci da abokan hadin guiwa ke yi.

Sanarwar, wadda Daraktan yada labaran Gwamna Lalong, Makut Macham ya fitar, ta yaba da kokarin da jami’an tsaro ke yi na ganin an ceto wadanda aka sacen.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply