Home Labarai Gwamnonin Nijeriya za su ƙara yin taro kan coronavirus

Gwamnonin Nijeriya za su ƙara yin taro kan coronavirus

146
0

Akwai yiwuwar gwamnoni 36 na Nijeriya za su ci gaba da tattaunawa a wannan satin kan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa da jihohin su.

Shugaban sashen yada labarai na kungiyar gwamnonin Nijeriya Abdulrazaq Bello Barkindo ya bayyana cewa an kira taron ne don tattauna yadda za a shawo kan matsalar faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya sanadiyyar barkewar cutar coronavirus.

Ya kara da cewa akwai yiwuwar gwamnonin su fito da matakan yadda za su tafiyar da kasafin kudin su, musamman kan abun da ya shafi biyan albashi, duba da faduwar farashin man, wanda hakan zai rage yawan kudaden shigar da suke samu, da kuma kason da gwamnatin tarayya ke turo masu.

Saidai ya ce ba zai yi wani karin bayani a kan wani batu ba, domin ba a bashi damar yin wata magana kan abun da gwamnonin ba su kai ga tattaunawa kan shi ba.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta sanar da rage kasafin kudin ta na bana, biyo bayan faduwar farashin man daga dala 57 ko wace ganga zuwa dala 28, biyo bayan yadda barkewar cutar coranavirus ta yi tasiri a kasuwar duniya, wanda hakan ke kara fargabar mawuyacin halin da za a shiga a nan gaba.

A taron da gwamnonin suka gudanar makon da ya gabata, shugaban kungiyar su Dr Kayode Fayemi, ya kafa wani kwamitin wucin gadi karkashin jagorancin gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai da zai duba halin da ake ciki tare da bada shawarar yadda za a magance matsalolin tattalin arziki da ke tunkarar kasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply